Akalla sama da mutum dubu 36, 000, ne na gamayyar kungiyoyin Malamai da na ‘yan kwadago suka gudanar da zanga-zangar lumana a Jihar Kaduna, duk da gargadi da barazanar da Gwamnatin Jihar ta yi a kan hana gudanar da zanga-zangar.
Tun da misalin karfe 6 na safiyar jiya Alhamis ne dakarun hadin gwiwar jami’an tsaro suka zagaye Sakatariyar ofishin kungiyar kwadago ta kasa, reshen Jihar Kaduna da ke titin Indifenda, domin ganin sun tarwatsa ‘ya’yan kungiyar da ke shirin gudanar da zanga-zangar.
Hadakar jami’an tsaron wanda suka hada da, sojoji, ‘yan sanda, jami’an tsaro na farin kaya, da dai sauran su. A kalla an jibge motocin yaki guda 10, motocin operation yaki guda 40, da kuma mashina akalla 15. A yayin da yake jawabi, Kakakin rundunar ‘yan sandar Jihar Kaduna, Aliyu Muktar, ya bayyana cewa, “ Mun zo wannan waje ne a bisa umurnin Kwamishinan ‘yan sanda domin mu tabbatar da cewa babu wanda za su gudanar da wani zanga-zanga a wannan waje.”
Kakakin rundunar ‘yan sandan ya kara da cewa,” A bisa wannan dalili ne kuke ganin mun tsaura tsaro a wannan waje domin gudun ko ta kwana.”
In ji Kakakin rundunar ‘yan sandar Jihar Kaduna, Aliyu Muktar. Sai dai duk da wancan doka da Kwamishinan ‘yan sanda ya bayar, za a iya cewa dokar ba ta yi tasiri ba, domin dubban masu zanga-zangar ne suka fito dauke da kwalaye mai dauke da taken rubutu iri daban-daban na gugar-zana da suka ga Gwamnatin Jihar Kaduna, karkashin jagorancin Malam Nasiru Ahmed El’rufai.
Kungiyar gamayyar ‘yan kwadagon Mata da Maza wanda kiyasin yawansu ya haura mutum dubu 36,000, sun karade galibin titunan Jihar Kaduna dauke da kwalaye da kuma ganye a hannuwansu suna tafiya suna rera wakokin nuna kyama ga Gwamnatin Jihar Kaduna, a bisa abin da suka kira da cewa, “babu wani mahaluki da zai kori ma’aikata sama da dubu 57 face wani mutum marar imani a cikin zuciyarsa”.
Duk da tsaurara jami’an tsaron da gwamnati ta yi, hakan bai hana masu zanga-zangar isa fadar gidan Gwamnatin Jihar Kaduna ba, a kokarinsu na ganin sun nuna matukar bacin ransu dangane da abin da Gwamnatin Jihar Kaduna, ke yi na ci gaba da sallaman ma’aikata a fadin jihar. Wasu da wakilinmu ya zanta da su, sun bayyana rashin jin dadinsu da irin salon mulkin Gwamnatin jihar Kaduna, wanda a cewarsu babu abin da hakan zai janyo illa karin marasa aikin yi a fadin jihar.
Wata mai suna Deborah Auta, wacce ta bayyana ma wakilinmu cewa, ta kwashe sama da shekaru goma 15 tana aiki a matsayin Akawu, yanzu an sallame ta ba tare da sanin dalilin sallamar ba. Shi ma wani mai suna Abubakar Bello Kauru, ya shaida ma wakilinmu cewa, ya na aiki ne da ma’aikatar hukumar kula da ruwa na Jihar Kaduna, wanda ya kwashe sama da shekaru 25 yana aiki da Gwamnatin Jihar, wanda shi ma korar ma’aikatar ta rutsa da shi, wanda cewarsa har yanzu bai san mene ne makomarsa ba, domin bai san wani aiki ba, face aikin gwamnati.
An dai gudanar da zanga-zangar cikin lumana da tsanaki, sai dai daga bisani jami’an tsaro sun sami nasar kama wasu Matasa ‘yan sara suka da ake zargin bata gari ne masu yunkurin tayar da zaune tsaye wanda da sun samu dama, abubuwa za su rincabe a Kaduna kamar yadda a baya ya sha faruwa. A halin da ake ciki kuma, shugaban kungiyar kwadago ta NLC, kwamared Ayuba Wabba, ya bayyana cewa ‘yan sandan ba su da ikon hana wani gangami matukar na lumana ne.
Idan ba a manta ba, a shekaranjiya Laraba kwamishinan ‘yan sandan Jihar Kaduna, ya kira taron manema labarai, in da ya bayyana cewa rundunar ta hana duk wani gangami a jihar saboda haka rundunar ba za ta amince da abin da kungiyoyin ke shirin yi ba a jihar. Sai dai a martanin da kungiyar ta mayarwa ga kwamishinan, ta ce tuni sun rubuta takarda ga Insifekta Janar na ‘yan sandan Nijeriya don sanar da shi yin wannan gangami, ba don neman izini ba.
Ya ce ba sa neman izinin kowa don yin gangami, domin tsarin mulkin Nijeriya ya ba su dama. A jawabin sa a wajen gangamin, shugaban kungiyar kwadagon na kasa, Kwamared Ayuba Wabba, ya bayyana cewa ba za su tsorata ba don ganin jami’an tsaro sun zagaye su. Ya ce aikin jami’an tsaron ne su kare su. A cewarsa, Gwamnan Jihar Malam Nasiru El-Rufa’i ya sanya an tare dukkan hanyoyin shigowa garin Kaduna, in da ake hana duk wani dan kungiyar shigowa Kaduna daga hanyar Abuja, Zaria, Jos da Birnin Gwari.
Bai kamata Gwamnan jihar ya manta da cewa a shekarar 2012 tare suka yi irin wannan gangami ba, in da suka bashi riga ya sa aka yi da shi. Ya ce ba za su suba ido ba ana korar ma’aikata ba tare da an bi ka’ida ba, in ji shi. Ayuba Wabba ya ci gaba da cewa ya tabbata ba hannun shugaban kasa a wannan magana ta korar ma’aikata. Domin jam’iyyarsa ta yi alkawarin samar da ayyuka miliyan uku ne duk shekara, ba korar ma’akata ba. Don haka ya yi kira ga shugaban kasa da ya sanya baki don ganin Gwamnan jihar Kaduna ya bi doka.
Ya ce tuni kotu ta baiwa Gwamnan jihar umarnin ya dakatar da korar ma’aikatan, amma Gwamnan ya yi watsi na wannan umarnin kotu din. Bayan masu zanga-zangar sun isa fadar gwamnatin jihar, Babban Jami’in Gwamnatin jihar Kaduna mai kula da sadarwa, Alhaji Sai’du Adamu ya amshe su a madadin Gwamnan jihar. Cikin jawabin da ya gabatar wa masu zanga-zangar, Hon. Saidu Adamu ya bayyana cewa Gwamnan ba ya nan, amma da zarar ya dawo zai isar da wannan sako nasu.
Ya ci gaba da cewa Gwamnatin jihar Kaduna tana son a bi ka’ida, don haka wadannan abubuwa za a duba, kuma za a yi duk abin da ya dace don cimma nasara. Kakakin gwamnatin ya ci gaba da cewa shi wannan abu na korar ma’aikata abu ne da aka riga aka cimma matsaya, hatta ita kanta kungiyar tana da masaniya a kai. Amma dai ya tabbatar masu da cewa zai isar da wannan sakon koken nasu ga Gwamnan da zarar ya dawo.
Batun korar malaman firamaren da aka ce ba su ci jarrabawar ‘yan aji hudu na makarantar firamare ba a kwanan baya, ya zama kamar cin-kwan-makauniya wanda ba a san ranar da za a kawo karshensa ba a nan kusa.